Iran na ci gaba da yin luguden wuta kan Isra’ila da sansanonin Amurka da kuma wasu ƙasashen gabas ta tsakiya, a wani martani ga hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai mata.
A Bahrain, mahukunta sun ce wuta na ci gaba da ci a babbar matatar man ƙasar, lamarin da ya sa kamfanin man ƙasar ya ayyana wata doka ta yarjejeniyar ƙin daukar asara tsakaninsa da abokan hulda, a yayin da aka shiga wani yanayi na bala’i.
A Isra’ila, an tabbatar da mutuwar mutum guda, da jikkatar wasu da dama sakamakon makamai masu linzamin da Iran din ke ci gaba da harbawa.
Shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Leo ya roki a kai zuciya nesa, yana cewa galibi tasirin yakin na karewa ne a kan ‘yan ba ruwana.