Iran ta samu damar fitar da kusan gangar danyen mai miliyan 73 daga yankin da takunkuman Amurka suka yi wa katanga cikin kusan wata guda, bayan da Washington ta ɗan sassauta wasu takunkumai da ƙuntatawar da ta sanya kan sayar da man ƙasar.
Daga ƙarshen watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuli, jiragen dakon mai na Iran da dama sun fara bayyana a ruwan gabashin Malaysia suna kan hanyarsu zuwa kasuwannin Asiya.
Kamfanin Kepler mai bibiyar jigilar makamashi ya shaida wa BBC cewa man da aka fitar a wannan lokacin na iya kai wa darajar kusan dala biliyan shida.
Sai dai duk da wannan gagarumar fitar da mai, rahotanni sun nuna cewa manyan masu sayen man Iran a China sun rage sayayyarsu.
Sai dai Amurka ta janye sassaucin takunkuman da ta yi wa Iran a ranar 7 ga Yuli, bayan ta amince na ɗan lokaci da sayar da ɗanyen man ƙasar tun daga 21 ga Yuni.”