Isra’ila Ta Bukaci A Cigaba Da Zama Sulhu Har Bayan Ramadan Kan Rikicinta Da Gaza

Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da bukatar Amurka na tsawaita wa’adin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni har zuwa bayan azumin Ramadan.

Gwamnatin Isra’ila ta sanar da cewa ta dauki wannan mataki ne domin bai wa jakadan da shugaba Donald Trump na Amurka ya nada kan al’amuran da suka shafi Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff, damar gabatar da sabbin matakai da shawarwari kan sulhun.

Ta kuma ƙara da cewa ta yi hakan ne domin bai wa al’ummar musulmi a Gaza damar gudanar da ibada har ma da Yahudawa da za su gudanar da bikin Passover a watan Afrilu.

Mai magana da yawun Hamas Hazem Qassem ya fitar da sanarwar cewa kungiyar ba ta amince da bukatar tsawaita wa’adin farko na yarjejeniyar ba.

Hamas Hazem ya ce, abin da Hamas ta ke bukata shi ne aiwatar da daftarin farko kamar yadda dukkanin bangarorin biyu suka amince.

A yarjejeniyar da aka cimma a watan Janairu, an bukaci dukkan bangarorin biyu dasu ajiye makamai har zuwa lokacin da za a kammala yarjejeniyar wanda kuma zai kawo karshen yakin da ake yi, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta DW Hausa ta wallafa.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda