Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta yaba wa Babban Bankin Najeriya (CBN) kan gyare-gyaren da take aiwatarwa domin dawo da daidaito, gaskiya da amincewa cikin tsarin hada-hadar kuɗi na ƙasar.
Sanarwar ta fito ne daga ofishin Daraktan Yaɗa labarai na Jami’ar ABU Malam Auwal Umar.
Jami’ar ta kuma bayyana gamsuwarta da yadda bankin ke jagorantar haɗin gwiwa tsakanin manufofin kuɗi da na kasafin kuɗi, a karon farko a matsayin matakin da ake ganin zai taimaka matuƙa wajen rage hauhawar farashin kayayyaki.
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ahmed, ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyara ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Olayemi Cardoso a Abuja.
Farfesa Ahmed ya kai ziyarar ne tare da Mataimakin Shugaban Jami’ar mai kula da Ci Gaba, Bincike da ƙirkire-ƙirkire, Farfesa Aliyu Rafindadi Sanusi.
“Ina so in yaba maka da tawagarka a taƙaice bisa muhimman gyare-gyaren da kuka aiwatar tun bayan da ka karɓi ragamar shugabancin bankin CBN.” Cewar Farfesa Ahmed.
Ya ce, Gwamnan CBN ya karɓi shugabancin bankin ne a wani yanayi mai matuƙar ƙalubale na tattalin arziki, wanda ya haɗa da matsin lamba a kasuwar canjin kuɗaɗen waje, hauhawar farashi, raunin amincewa da kuma manyan matsalolin tattalin arziki.
Ahmed ya ƙara da cewa, Jami’ar ABU ta fahimci irin ƙarfin hali da Gwamnan CBN ya nuna wajen gudanar da gyare-gyaren da nufin dawo da daidaito, gaskiya da amincewa cikin tsarin kuɗi.
Ya bayyana gyare-gyaren da aka yi a kasuwar canjin kuɗaɗen waje, ƙoƙarin ƙara ƙarfafa ajiyar kuɗin waje da amincewar kasuwa, sake ƙarfafa jarin bankuna da kuma sabunta mayar da hankali kan ingancin manufofin kuɗi a matsayin muhimman matakai a kan turba madaidaiciya.