Ƙungiyar dalibai (SUG) ta Jami’ar Ibadan ta tabbatar da sace wata ɗaliba yar aji uku, wato level 3, a fannin koyon ilimin shari’a yayin da ta ke dawowa daga wani taro na addini da aka gudanar a Jihar Imo.
Shugaban SUG, Temidayo Adeboye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Ibadan ranar Juma’a, inda ya ce ɗalibar mai suna Tomisin an yi garkuwa da ita tare da wasu mutum bakwai.
A cewarsa, Tomisin na tafiya tare da Babban Daraktan ƙasa na ƙungiyar Scripture Union Student Fellowship, Uwem Cosmos, da sauran mahalarta taron.
Rahotanni sun nuna cewa suna kan hanyar komawa Ibadan ne bayan halartar taron Scripture Union National Conference da aka gudanar a Camp of Faith, Okigwe a Jihar Imo.
Adeboye ya ƙara da cewa rashin ganin ɗalibar ya bayyana ne bayan ta kasa halartar jarrabawar da aka tsara mata a ranakun Litinin da Talata.
Ya ce wata ɗaliba daga Sashen Kiɗa da ta halarci taron ta riga ta dawo lafiya.
A nasa ɓangaren, Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Misis Joke Akinpelu, ta tabbatar da cewa jami’ar na sane da lamarin, sai dai ba a sanar da ita tafiyar ba tun farko.
A cewarta, lamarin ya faru ne a ranar Asabar, tana mai cewa ɗalibar ita kaɗai ce daga UI da aka tabbatar an yi garkuwa da ita, ba takwas ba kamar yadda rahotanni ke yawo.
Ta ƙara da cewa ɗalibar ta bar jami’a ba tare da sanar da hukuma inda za ta ba