Majalisar dokokin jihar Katsina ta jinjina wa tsohon shugaban ƙasar nan na mulkin soja, Gen. Ibrahim Babangida mai ritaya, bisa hangen nesan sa na samar da jihar.
An ƙirƙiri jihar ne a daga jihar Kaduna a ranar 23 ga watan Satumbar, 1987 a lokacin mulkin Gen. Ibrahim Babangida.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani saƙon taya murna da sakataren yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar ya fitar, Malam Aminu Magaji wanda ya ce;
Shugaban majalisar, Alhaji Nasir Yahaya, yana taya al’ummar jihar murnar ganin wannan rana ta tuna wa da kafa jihar a shekaru 36 da shuka wuce.
Tare da jinjina musu bisa ƙoƙarin zama lafiya da haɗin kai a tsakanin juna ba tare da la’akari da addini da ƙabila ba da sauransu.
Sannan ya yaba wa gwamnan jihar, Dikko Radda, bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da tsaro a jihar tare da alƙawarin mara masa baya a kodayaushe.