Dan gane da aikin Hajjin bana dai, rahotonnin daga Jamhuriyar Nijar na tabbatar da cewa Jirgin ƙarshe na maniyyatan kasar ya isa ƙasa mai tsarki wato Saudiyya.
Wanda alƙaluma suka nuna cewa Jimillar mutune 15,891 ne za su yi aikin Hajji na bana daga Jamhuriyar ta Nijar .
Sai dai akwai wasu mutane da dama da ba za su damar zuwa gudanar da ibadar ba duk da cewa sun biya kuɗinsu ta hannun wasu kamfanonin shirya aikin hajji da Umarah.
Ana samun matsalolin rashin samun tafiyar maniyyata, sakammakon wasu dalilai mabambanta, a wasu ƙasashe da suka haɗa da Nijeriya, wanda hakan yake baƙanta ran maniyyata.