Mahukunta Masallatan Alfarma na kasar Saudiyya, sun sanya Hausa a cikin jerin harsuna 20 da za a yi amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arafa ta bana. Daidai lokacin da mahajjata a sassan duniya suka fara aikin sauke farali na bana a kasar mai tsarki.
A shekarun bayan nan dai an rika fassara hudubar ranar Arafa cikin harsuna daban-daban, inda kusan shekaru uku da suka gabata harshen hausa ya samu shiga.
A wannan Lahadin ne ake soma aikin hajjin a Makkatul Mukarrama cikin yanayin zafi, inda dubun dubatar musulmi suka halarci aikin hajjin farko da aka baiwa kowa dama a masarautar tun bayan barkewar cutar Covid-19.
Sama da mahajjata miliyan biyu daga kasashe 160 ne ake sa ran zasu gudanar da Ibadan na bana a birnin mafi tsarki ga addinin musulunc a yammacin Saudiya, bayan shafe shekaru uku ana takaita adadin masu halarta saboda barkewar annobar korona.