Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 ya yi hatsari a kogin Gumoda da ke Nahuche, Karamar Hukumar Taura Jihar Jigawa, inda mutune biyar suka rasa ransu.
Malam Haruna Wada Adamu wanda ɗan garin ne, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin inda ya bayyana mamatan a matsayin mutanen kirki kuma masu amfani a cikin al’ummarsu.
Rahotanni sun ce lamarin ya rutsa da mutane 20 ne, 15 daga cikinsu sun tsira amma biyar sun amsa kiran mahaliccinsu.
- Akwai ‘Yan Siyasar Dake Taimakawa Masu Zanga-Zanga – Kashim Shettima
- Ruwa Ya Karya Gada A Yankin Katagum
A wata sanarwar da mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Reshen Jihar Jigawa Lawal Shisu Adam ya ce bayan samun kiran gaggawa daga yankin, kuma sun bada iya gudunmawar da ta dace, sai dai duk da wannan kokarin nasu, fasinjoji biyar sun rasa ransu.
Wanda suka rasa ran nasu sun hada da Abdurra’uf Muh’d, mai shekara 20, Sulaiman Ali, mai shekaru 20, Shafi’u Mohd mai shekaru 25, Ado Nafance mai shekaru 75, da kuma Alasan Muh’d, mai shekaru 16 duk daga garin Nahuche Karamar Hukumar Taura.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ya bayyana alhininsa da kuma sakon jaje ga iyalan mamatan.
Da yake ƙarin bayani, jagora kuma mai fafutukar kawo wa yankin cigaba, Malam Haruna Wada Adamu ya ce, za su yi amfani da Ƙungiyar su wurin inganta rayuwar jama’arsu.
Ya ce nan ba da jimawa ba za su fitar da tsari tare da haɗin guiwar shugabannin kan yadda za a riƙa shiga jirgin ruwan musamman a wannan lokaci da ake ci-gaba da samun ruwan sama.
Alhaji Nasir Usman wani ɗan siyasa da ya fito daga garin ya bayyana alhininsa bisa faruwar lamarin, ya kuma buƙaci gwamnatin jihar ta dubi garin da ke tsohon tarihin siyasa da idanun Rahama, wurin kawo hanya da jiragen ruwan zamani domin inganta rayuwar al’ummar garin.