Ministan sufurin jiragen sama na ƙasar, Festus Keyamo ya tabbatar da cewa jirgin sojin ƙasdar mai saukar ungulu ya faɗi a Igbokoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ilaje ta jihar Ondo.
Keyamo ya ce jirgin na ɗauke da mutum 32, da suka haɗa da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai.
Hatsarin ya haifar da firgici a yankin da ke gabar teku, yayin da aka tura jami’an agajin gaggawa da na tsaro zuwa yankin.
Wani mazaunin yankin, Olorunlola Oluwafemi, ya shaida wa BBC cewa ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya lokacin da mutanen yankin suka ji “ƙara mai ƙarfi kamar tsawa.”
Ya ce bayan sun fahimci cewa ba tsawa ba ce, “mun fita waje inda muka gano cewa kamar jirgin sama ne.”
Ya ƙara da cewa hayaki na tashi daga wurin da jirgin ya faɗi.
A cewar Oluwafemi, jirgin ya yi hatsarin ne kusa da wani daji da ke makwabtaka da sansanin rundunar sojin ruwan Najeriya na FOB a Igbokoda.
Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun tura jami’ai zuwa yankin, inda ake ci gaba da aikin nema da ceto.