Daga: Siraj Na’iya Kududdufawa
Tsohon ɗan wasan ƙungiyoyin ƙwallon kafa, Sporting CP da Manchester United da Real Madrid, da Juventus wato Cristiano Ronaldo ya yi wasu kalamai bayan ƙungiyarsa ta Al Nassr ta zazzaga kwallaye a gasar Saudi Pro League.
Ya yi kalaman ne bayan da kungiyar sa ta Al Nassr ta samu nasara a wasanta na ranar Litinin da gagarumin rinjaye inda Ronaldo ya zura kwallaye guda 2.
Bayan zura kwallayen ne Ronaldo ya ci gaba da jan zaransa na dan wasan da ya fi kowa yawan zura kwallaye tunda aka kirkiri kwallon kafa inda ya zura 923.
Ronaldo ya kwashe shekaru 39 a duniya amma ya na yin abubuwan mamaki tamkar dan shekaru 25, kwallayen da ya jefa guda 923, ya jefa guda 463 tun yana kasa da shekaru 30, sannan ya jefa guda 460 bayan ya haura shekaru 30.
Kalaman da Cristiano Ronaldo ya yi a wannan safiya ta Talata bayan ya samu nasarar jefa kwallaye, inda ya ce:
“Duk da shekarun da na kwashe ina sharafi na, labari da duk wani tarihi da zan kafa rubutacce ne, na san na kafa tarihi ko yanzu, kuma ba zan rataye takalmana ba, sannan ko yanzu na daina fafata wasan kwallon kafa ba zanyi nadama ba, amma idan na daina tabbas za a tausayamin, sabo da har yanzu ina kan sharafi na”.
- Masana Su Fara Hasashen Lokacin Tashin Duniya
- Jijjiga: Ciwon Da Ya Daɗe Yana Yi Wa Mata Kisan Mummuƙe
Tauraruwar Ronaldo dai naci gaba da haskawa a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake kasar Saudiyya, inda ya jefa kwallaye masu yawa.