Iran da Saudiyya sun amince da sake kulla huldar diflomasiyya tare da bude ofisoshin jakadanci bayan kwashe shekaru ana takun-saka tsakanin kasashen biyu, ciki har da wani mummunan hari da aka kai matatar mai ta Saudiyya da ake dangantawa da Tehran.
Yarjejeniyar, wacce aka kulla a birnin Beijing cikin wannan makon, ana ganin wata babbar nasara ce ta diflomasiyya ga SIN, yayin da kasashen Larabawa ke ganin Amurka sannu a hankali za ta fice daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an diflomasiyya ke kokarin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru ana gwabzawa a kasar Yemen, rikicin da kasashen Iran da Saudiyya ke da hannu a ciki.
Kasashen biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan yarjejeniyar a ƙasar Sin, wacce da alama ita ce ta kasance mai shiga tsakanin ƙasashen biyu.

Kafofin yada labarai na kasar Iran sun nuna Ali Shamkhani, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran, tare da wani jami’in Saudiyya da Wang Yi, babban jami’in diflomasiyyar kasar Sin a yayin tattaunawar.
Sanarwar haɗin gwuiwar ta yi kira da a sake kulla alaka da kuma buɗe ofisoshin jakadancin nasu nan da watanni biyu masu zuwa.
An dai yi takun saka tsakanin Iran da Saudiyya, inda Masarautar ta yanke hulda da Iran a shekarar 2016 bayan da masu zanga-zanga suka mamaye ofishin diflomasiyyar Saudiyya. A kwanakin baya ne Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wani fitaccen malamin Shi’a wanda ya janyo zanga-zangar.
A cikin shekarun da suka gabata, tashin hankali ya kaure a Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da manyan kasashen duniya a shekarar 2018.
An zargi Iran da kai wasu hare-hare a wancan lokacin, ciki har da wanda ya shafi Saudiyya a shekarar 2019, abin da ya kai ga rage danyen man da Saudiyya ke hakowa na ɗan wani lokaci.