Kano: Hukumar KAROTA za ta fara kama yara masu tuka baburan a-daidaita-sahu

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, za ta ci gaba da kama yara masu tuƙa baburan a-daidaita-sahu waɗanda ba su kai shekara 18 ba.

Shugaban Hukumar KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka, a lokacin da yake karbar baƙuncin gamayyar ƙungiyoyin a-daidaita-sahu na jihar nan, a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mansur Tanimu

Injiniya Faisal ya ce Hukumar KAROTA ba za ta amince da bai wa ƙananan yaran da ba su kai shekara 18 tuƙin a-daidaita-sahu ba.

Sannan, Hukumar ta ce ba za ta yarda da yin amfani da waya a lokacin tuƙi ba, da kuma ɗaukar kaya fiye da kima a cikin a-daidaita-sahu

Sai dai gamayyar wasu ƙungiyoyi a Kano sun roƙi gwamnatin jihar da ta samar da makarantar da  za ta bayar da horo ga matuƙa a-daidaita- sahun faɗin jihar nan, domin hakan zai taimaka wajen rage aikata laifukan tuƙin da ake gani a kan titunan jihar nan.

Post masu alaƙa

2027: ADC ta zargi Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki

Zaɓen 2027: Rundunar yan sanda jihar Kano ta ba da tabbacin tsaro,tare da yin gargaɗi kan yada labaran ƙarya

NDLEA Ta Kama Mutane 1,860, Ta Kwace Ton 5.4 na Miyagun Ƙwayoyi a Kano.