• Home  
  • Kano: INEC ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin kotu
- Labarai

Kano: INEC ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin kotu

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

Kano: INEC ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotu

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

An tabbatar da hakan ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Suleiman Alƙali, shugaban sashen shari’a na hukumar a Kano.

Suleiman Alƙali ya ce, Hedikwatar hukumar INEC ta umurce shi da cewa a hukumance ba ta da wani dalili na ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.

Shin ya dace INEC ta ɗauki irin wannan mataki a daidai lokacin da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka ƙara? Ina ma’anar hakan ga ɗaukaka ƙarar gwamnan jihar Kano? Ba ita INEC ke da alhakin kare abinda ya faru a shari’ar sauraron ƙarar zaɓen gwamnan jihar nan ba?

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000