MA’aikatar Lafiya ta Kano ta musanta zargin ɓarkewar cutar kyanda a wasu ƙananan hukumomin Kano.
Wannan na zuwa ne cikin wani jawabi da jami’in hulɗa da jama’a na sashen kula da lafiyar a’umma da kula da cututtuka, Dr. Imam Wada Bello, ya yi kan ɓarkewar kyanda a Kano.
Da yake ƙaryata wannan batu a ranar Laraba, Dr. Imam, ya ce, akwai matakai da ake bi kafin a tabbatar da ɓarkewar cuta wanda ya haɗa da yin bincike a ɗakin gwajin da kuma auna girman matsalar da adadin mutanen da suka kamu da wannan cuta.
Ya ce sam a nan Kano ba a bi waɗancan matakai ba da zai sa a ayyana ɓarkewar kyanda a jihar nan, inda ya buƙaci al’umma da su yi watsi da wancan labari saboda babu bincike na masana lafiya a kansa.
Daraktan ya ce a shirye suke wajen ɗaukar dukkan wasu matakai wajen tabbatar da ɓarkewar kowacce irin cuta a Kano.
Kuma ya ce ma’aikatar tare da sashen kaki agajin gaggawa na ma’aikatar a ƙananan hukumomi 44 da ake da su a shirye suke wajen ɗaukar matakin da ya kamata.