Gwamnatin Saudiyya ta hana alhazai fita jifar shaidan daga karfe 11 na safe zuwa 4 na yamma saboda tsananin zafi.
Sanarwar da aka tura wa hukumomin aikin hajjin kasashen duniya ta ce ma’aikatar ta umarci jami’an tsaro da su dakatar da duk wani alhaji ko hajiya da suka bijire wa wannan umarni.
Ana tunanin hukumar ta dauki wannan mataki ne sakamakon mutuwar wasu alhazai a ranar Lahadi da aka fara jifa.
- Sanata Barau I. Jibril ya mika sakon barka da sallah ga ‘yan Najeriya
- Sallah: Gwamnan Kano ya jaddada aniyarsa ta cigaba da ayyukan raya jihar
Ana gudanar da aikin hajjin bana a cikin yanayi na tsananin zafi da ya haura maki 40 a ma’aunin rana.
Hukumomin hajji da na lafiya sun ja hankalin alhazai da su yawaita shan ruwa da amfani da lema in suna tafiya acikin rana.
Jami’an sun bada shawarar a gujewa shiga rana a yayin ibadar aikin Hajji dam kuma yayin zaman mahajjata a kasar Saudiyya.