Kano: Za mu hukunta masu zubar da shara a wuraren da ba su kamata ba ~ Ahmadu Haruna Zago

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli  ta jihar Kano  Ahmadu Haruna Zago, yace hukumar sa za ta yi amfani da sashen dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da ba su kamata ba a jihar nan.

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai yayin da  ma’aikatan hukumar suke tsaka da aikin kwashe sharar dake fagge, ‘yan Alluna.

Dan zago yace abin takaici ne yadda wasu suke bin tsakar dare suna jibge shara akan titunan jihar nan da wuraren da basu dace ba,  musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.

A bayanansu tunda farko mazauna kasuwar ta Fagge ‘yan Alluna, sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan, Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa  ya kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.

Post masu alaƙa

Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.

Tinubu ya taya ‘yar Gombe murnar lasha gasar musabaka ta duniya

Mutanen da suka mutu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48