Kasa Hada Malamai A Dandamali Daya Ke Kawo Baraka: Dakta Sa’id Dukawa.

Tunzurawar da wasu mabiya ke yi wa Malamansu na addini  na kara  jawo rarrabuwar kai  tsakanin Malamai masu bambancin fahimta.

Wannan lamari na tunzira wasu malamai da wasu mabiyansu ke yi yayin da suka hau kan munbari, ba sabon abu bane, kuma hakan na sanya malaman su riƙa sukan ‘yan’uwansu malamai.

Al’ummar gari na alakanta hakan da rashin ilimi daga wasu mabiyan , yayin da wasu suka bayyana cewa yawancin masu yin hakan basa zama a gaban malaman su koyi karatu.

A bangare guda kuma wasu sun ce akwai malaman da sune suke sukar wasu malaman wadanda akidar ba iri daya bace, shi yasa ake samun mabiyan suke sukar wasu malaman.

Haka zalika wani Dattijo mai suna Ma’azu Adamu , ya ce son nuna griman ilimi da son zuciya ne ke haifar da hakan, kuma idan wani malami ya yi wani abu bisa sabawar wata fahimta, sai a dinga sukarsa ta hanyar kafofin sada zumunta maimakon a sanar dashi , ta hanyar data dace wanda hakanne musabbabin sukar junan.

Sakataren zauren hadin kan malaman Kano, Dakta Sa’id Ahmad Dukawa, ya bayyana cewa matsalar ta samo asali
ne sakamakon rashin dandamalin haduwa waje guda, kuma suna iya bakin kokarinsu domin ganin an dinke dukkan wata baraka dake tsakanin Mabiya malaman da suke sukar juna.

Dukawa ya ce a lokacin da tashon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekaru, ya hada malaman jihar, a majalissar Shura ta gwamnati wadanda suka dinga haduwa suna tattauna al’amuran jama’a tare da kawo hujjoji kuma a dauki matsaya guda daya, inda aka samu karancin sukar juna a wancan lokacin.

Ya kara da cewa a shekarar 2012  suka kafa zauren hadin kan malaman Kano, an samu dandamali da malamai na kowanne bangare da suke haduwa , su tattauna matsalolin al’umma tare da daukar matsaya guda daya, inda ya tabatar da cewa duk wanda yake zuwa da wahala a same shi cikin masu sukar juna.

Haka zalika , Dakta Dukawa, ya ce zauren hadin kan malaman ya kafa kungiyar tallafi wadda ta ke nemowa daga mawadata ta rabawa mabukata musamman lokutan da aka samu tashin hankali harma wasu su rasa mahallansu.

‘’ da tafiya neman taimakon da tattarashi da tsara yadda za a  kai taimakon da tafiya aje kai taimakon duka malaman na kowanne bangare suna haduwa su yi, kuma wannan yana rage matsala sosai da wahala kaga irin wadannan malaman wadanda kake bayar da misali da su’’ Dakta Sa’id Ahmad Dukawa’’.

Sai dai ya ce kusan kowanne wata akwai taron bita a jami’a, inda ake karawa juna ilimi kuma duk wanda yake halatta ba za aji cikin masu sukar juna ba.

Sannan ya kara da cewa , Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na ii, ya tara malamai tare da tattauunawa mai zurfin kan yadda za a samar da doka ta tafiyar da iyali da yadda za a  inganta ilimin allo da yadda za a rage talauci a cikin al’umma, kuma na tattaro malaman daga kowanne bangare.

‘’ wannan tattaunawar tana taimakawa ya zama an fahimci juna, kuma zaka tarar babu sukar juuna sannan tana fitar da matsaya guda daya , wadda idan babu irin wannan jagorancin to kowanne malamai zi fadi fahimtarsa wani kuma ya fadi sabaninta sai na farko ya zaci raddi wani yayi masa sai ya mayar masa, shima sai ya zaci wani yaki ya dauro masa sai shima ya mayar masa, to anan magoya bayan suke shigowa anan suke tunzira su’’.

A karshe ya ce duk yadda za a samar da haduwar malamai kan al’amuran da suka shafi jama’a da addini su tattauna sannan su fitar da matsaya guda daya to za a samu nasarar magance matsalar baki daya.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda