Kasar Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da ECOWAS sun nuna rashin jin dadinsu game da yunkurin cigaba da tsare habbararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.
Sun bayyana cewa yin hakan ka iya cigaba da munana halin da ake ciki a kasar.
A cikin satin da ya gabata ne shuwagabannin sojojin da suka yi juyin mulki ne suka tabbatar da shirin da suke na aike wa da shugaba Bazoum kotu bias zargin cin amanar kasa da cin dunduniyar jami’an tsaron kasar.
Mai magana da yawun gwamnatin Amurka, Vedant Patel, ya ce sun kadu jin matakin da sojojin suka dauka na mika Bazoum kotu.
Inda ya bayyana hakan a matsayin rashin adalci wanda hakan ba zai samar da kyakkyawar alakar da sojojin ke son samu ba.
Ita kungiyar ECOWAS ta yi Alla-wadai da yunkurin da sojojin na Nijar ke yi na tuhumar Bazoum da cin amanar kasa.