Ƙasar Birtaniya da taƙwararta ta Faransa sun yi wata ganawa domin tattauna game da matsalar baƙin haure a iyakokin ƙasarsu tare da duba abin da suke kashewa a iyakokin ƙasar tasu.
Tuni dai Macron ya tarbi Sunak a fadar Elysee, bayan firaministan ya tafi Paris ta jirgin kasa daga Landan. Kuma da yammacin yau ne ake sa ran gudanar da taron manema labarai.
Wannan dai shi ne taron farko da Birtaniya da Faransa ke yi cikin shekaru biyar, bayan da Sunak ya zama firaminista a watan Oktoba, biyo bayan saukar Liz Truss da Boris Johnson.
An tsara tattaunawar ne don samar da wata yarjejeniya da za ta dakile kaura daga Faransa, inda Sunak ya yanke shawarar dakile dubunnan masu neman mafaka da ke tsallaka wa ƙasar ta tsibirin da ake kira da Channel, yayin da ita ma Faransa ke neman yadda za a kare kan iyakarta.
Biritaniya dai na biyan Faransa ne domin taimaka mata wajen gudanar da aikin sintiri a tsibirin, kuma yarjejeniyar da za a tattauna a kai za ta mayar da hankali ne kan kara yawan albarkatun da ake turawa domin samar da tsaro kan iyakar, tare da samar da kudaden da za a yi amfani da su na tsawon shekaru.