Kashim Shettima ya isa Bauchi halartar jana’izar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa jihar Bauchi domin halartar janaizar fitaccen malamin addinin nan da ya rasu a jiya Alhamis, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya sami tarba ne daga gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da kuma na jihar Neja Umar Bago wanda tuni shi ma ya isa jihar.

Ana sa ran nan gaba kaɗan ne za a yi jana’izar marigayin a wani filin idi da ke jihar Bauchi, kafin a kai shi makwancinsa da ke babban massalacinsa.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.