ADC ce kawai za ta ceto Najeriya – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce jam’iyyar ADC ce kawai za ta iya ceto Najeriya daga halin da take ciki na matsalar tsaro da tattalin arziki.

Yayin da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar ofishin jam’iyyar a jihar Taraba a ranar Asabar, Atiku ya ce ya shiga jam’iyyun APC da PDP a baya kuma ya fahimci ba za su iya fitar da Najeriya daga halin da take ciki ba.

A cikin makon nan ne dai tsohon ɗan takakarar shugaban ƙasar ya yanki katinsa na ADC, lamarin da ke alamta shigarsa jam’iyyar a hukumance.

Atiku Abubakar ya kuma yi kira ga mutanen Taraba su fito su shiga jam’iyyar ta ADC, idan har suna son ”ceto tsaro da tattalin arzikin Najeriya”.

”Ina kira ga mata da matasa, su fahimci cewa muna yin wannan domin inganta makomarsu”, in ji Atiku.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya