Wata kotun majistiri dake zamanta a Hadejia jihar Jigawa ta bayar da umarnin kamo wani jami’in hukumar tsaron farin kaya, DSS, mai suna Ifeanyi Festus, bisa zarginsa da sace karamar yarinya da tursasa mata sauya addininta zuwa kiistanci tare da cin zarafinta ta hanyar lalata.
A cewar kotun, ana zargin jami’in da sace Walida Sani, wata ƙaramar yarinya Musulma daga Jihar Jigawa, inda ya tilasta mata sauya addini sannan ya riƙa yin lalata da ita, abin da ya haifar mata da ɗaukar juna biyu.
Kotun ta bayar umarni ga kwamishinan yan sandan jihar Jigawa da mataimakin darakta janeral na hukumar DSS ko wani jami’I dake aiki a karkashinsu, su gaggauta kamo wanda ake zargin don fadada bincike kan lamarin.
Haka zalika kotun ta umarci hukumar DSS ta gaggauta mayar da yarinyar zuwa hannun iyayen ta ba tare da bata lokaci ba.
Rahotanni sun kuma nuna cewa an kai yarinyar wani asibiti a Abuja domin yi mata wani aikin jinya sakamakon matsalolin lafiya saboda ƙarancin shekarunta.
- Gobara ta ƙone dukiyar N15m a Gusau
- Majalisar Dattawan Amurka za ta rage ikon Trump kan sha’anin tsaro
Ana sa ran wannan mataki zai buɗe hanya gudanar da cikakken bincike na shari’a, yayin da jama’a da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke sa ido kan yadda lamarin yake tafiya.
Lauyan iyayen yarinyar, barista Hussaini Sani , ya bayyana cewa za su jira suga anbi umarnin da kotun ta bayar , amma idan ba abi ba za su dauki mataki nagaba.
Masana shari’a da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana cewa wannan lamari ya shafi ‘yancin addini da kare yara da kuma mutuncin ƴa mace, tare da kira ga hukumomi da su tabbatar da cikakken bincike ba tare da son rai ba.
Yayin da ake jiran ci gaban shari’ar, ‘yan Najeriya da dama na sanya ido kan lamarin, suna fatan ganin gaskiya ta bayyana da adalci , kuma a ɗauki matakan kariya masu ƙarfi domin hana sake faruwar irin wannan ta’asa ga yara da mata masu rauni.
