Kotu Ta Daure Almajiri Dan Shekaru 14 Saboda Batan Kayan Dan Kasuwa.

 

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

 

Wata kotun Shari’ar addinin musulinci  dake zamanta a bayan fada karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi, ta yankewa wani almajirin mai suna ,Khalid Yahaya, dan shekara 14  hukuncin daurin shekara daya tare da biyan diyyar naira dubu dari hudu da arba’in da biyar (445), sakamakon samun da laifin sace kayan wani dan kasuwa mai suna ,Alhaji Sambo Wudil, a kasuwar Gadarmaiwa.

a hukuncin da ya yanke lkalin kotun mai shari’a, Malam A. Abdulhamid, ya bukaci almajirin ya biya kudin Kaya naira dubu 400 da kudin kotu dubu 30 da kuma kudin ‘yan sanda naira dubu 15, saboda abin da ya kira almajirin ya yi sakaci an dauke buhun hulunan da hirami wanda ,Sambo Wudil, ya dora wa almajirin Khalid zuwa motar da su ke daukar kayan sa zuwa gida daga kasuwar.

Kamar yadda Almajirin Khalid ya bayyana wa wakilinmu cewa a kullum Yana daukar dakon kayansa ya kai Mota, idan ya ba masu Lodi sai ya tafi sai wani mako idan yazo yake hada kudin ya bashi.

Amma a kwanaki bayan ya ba masu mota kayan ya tafi satin gaba sai mai kayan yace masa bai ga buhun kayansa ba.

Malamin Khalid wanda ke kawo shi kotu mai suna Alaramma Sha’aibu Inuwa, ya bayyana cewa Khalid maraya  ne da ke Kano,  Amma saboda babansa ya rasu ‘Yan uwa suka ba shi amana don ya koya masa karatu don haka suka zo Gadarmaiwa wannan matsalar ta faru a lokacin da yake  neman abinci.

Malam Sha’aibu ya kara da cewa ana cikin Shari’ar, ita ma mahaifiyar Khalid ta rasu, saboda dama bata da lafiya,
Ya ce a yayin zaman Sharia na farko Alhaji Sambo ya ce kayansa ya kai naira dubu 200.

 

Don haka Malam Sha’aibu ya ce za a nemi taimako a biya shi, amma daga bisani a zama na gaba ya ce ya kara lissafi kudin kayan sun kai naira dubu 600, don haka lamarin sa ya fara kawo tsaiko a Shari’ar, aka ci gaba da kiran shaidu guda uku yadda ya kara cewa kayansa sun kai naira milyan daya da rabi saboda cikin kayan akwai hulunan dara guda goma.

Alkali A. Abdulhamid,  ya bukaci dan kasuwar ,Sambo ya ji tsoron Allah amma ya ce kudin kayansa kenan,  daga bisani Alkalin ya bukaci Alhaji Sambo ya yi rantsuwa amma ya ki amincewa.

Hukunci ya dawo kan almajirin Khalid da cewa  zai yi rantsuwa idan shi ya dauke kaya rantsuwa zata kama shi kuma ya amince zai rantse.

Amma a ranar yanke hukunci Alkalin ya zartas da daure shi shekara guda da biyan dubu dari hudu da arba’in da biyar 445.
Daga karahe malamin ya ce shi ba shi da hanyar biya wa almajirin tarar saiko gwamnati ta tafi da shi, don haka aka kawo shi gidan kangararrun yara na Remand Home da ke Bauchi saboda karancin shekaru don yin zaman hukuncin.

A ranar 26/6/2025 wakilinmu a Bauchi ya je gidan wakafin ya zanta da Khalid Mai kananan shekaru Wanda ma’aikatan suka ce tun ranar da aka kawo shi , yake kuka baya cin abinci saboda alamu sun nuna bai taba shiga wannan yanayi ba.

Ya shaida wa wakilinmu cewa tun ranar da aka kai shi gidan sun fi 40 a ciki, Amma kullum kangararrun yaran bugunsa su ke yi ba dare ba rana wai ana masa service.

Don haka wakilinmu ya gayyaci wata kungiyar kare hakkin kananan yara da wani bawan Allah, suka kai wa Yaron dauki ta hanyar hada taimakon kudin da aka shigar da kara zuwa kotun daukaka kara zuwa Upper Kafin Madaki don ci gaba da Shari’ar.

Yanzu dai kotun ta bayar da belin Almajirin Khalid, kuma tuni malamin sa ya tafi da shi ana jiran lokacin da za a karbo kwafin Shari’ar Daga Ningi don ci gaba da sauraro.

Don haka Malam Sha’aibu Inuwa ya bukaci kungiyar matan Gwamnoni da na lauyoyi da masu kare hakkin yara su taimaki wannan yaro maraya don ceto shi Daga hannun dan kasuwar saboda gani ya ke Yi za a yi ta neman taimakon tara masa wannan kudin, alhali a yanzu kudi yana da matukar wahala.

Malam Sha’aibu ya kara da cewa lokacin da aka bukaci dalilin da Alhaji Sambo ya ke kara yawan kudin kayansa ya ce ‘yan sanda ne cikin bayanan su ta bakin Mai Shigar da kara insfekto Nura ya Kara kudin da ake tuhuma.

A gefe guda kuma shaidun Sambo Wudil sun ce kayan da yake sayarwa babu hula dara sai ko idan ana so kudi ake ba shi ya kawo saboda tsadar ta.

Daga karshe hatta shaidun sa da ‘yan sanda da mutane da dama sun roki ya yi hakuri saboda hannun da ya kirga riba wata rana dole ya kirga asara amma yace shi yana so daina ganin Yaron a waje shi ne bukatar sa .

Yanzu dai ana jiran ranar da kotun daukaka kara ta Upper Kafin Madaki karkashin Alkali Adamu Bello zata fara sauraron karar.

 

Post masu alaƙa

Ƙungiyar muhaɗu mugyara ta bayyana Muhasa TVR a matsayin kan gaba wajen gyaran tarbiyyar al’umma.

Fursuna ya tsere bayan hatsarin motar jami’ai a Yobe

Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda