Babbar kotun jihar Kano, lamba 18 karkashin jagorancin mai shari’a Fatima Adamu, ta yanke hukucin kisa ta hanyra rataya ga mutanen da aka samu da laifin fashi da makami da kuma kisan kai.
Wadanda aka samu da laifin sun hada da, Amir Zakariyya Shamaki da kuma Aliyu Usaini Sheka.
An gurfanar da su ne da tuhumar aikata fashi da makami da kuma kisan kan malamin jami’ar North West Kano, mai suna Buhari Imam, bayan sun kwace wayarsa, wanda lamarin ya faru a ranar 11 ga watan Yuni 2025.
- An Kama Dan Uwan Nnamdi Kanu Da Lauyansa —Sowore
- Gwamnonin Kano Da Katsina Da Jigawa Sun Shiga Yarjejeniyar Bunƙasa Lantarki.
Lauyan gwamnatin jihar Kano , Barista Lamido Abba Soron-Dinki, ya gabatar da shaidu uku , yayin da wadanda aka gurfanar din suka Barista Haruna Sale Zakariyya, ya tsaya musu wajen bayar da kariya.
Kotun ta bayyana cewa ta gamsu da hujjojin da lauyan gwamnati ya gabatar sannan ta yanke musu hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari kan laifin hadin baki da daurin shekaru 10 na fashi da makami da kuma hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe marigayi Buhari Imam.