• Home  
  • An Kama Ɗan Fashi Da Miliyan 4.9 A Kano
- Babban Labari - Labarai

An Kama Ɗan Fashi Da Miliyan 4.9 A Kano

‘Yan Sanda sun kama ɗan fashin ne da safiyar Talata.

Nasarawa: Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ta Kame Masu garkuwa da Mutane 26

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya A Jihar Kano, ta sanar da kama wani babban ɗan fashi da makami.

Mai magana da yawun rundunar a Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana cewa sun kama mutumin da ake zargin ƙasurgumin ɗan fashi ne.

An sami ɗan fashin da kuɗi kimanin Naira miliyan 4 da dubu ɗari 9 da tamanin.

Kazalika an samu a samu bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da kuma alburusai 47.

‘Yan Sanda sun yi nasarar kama ɗan fashin ne da ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata ne.

SP Haruna Kiyawa ya bayyana kama ƙasurgumin ɗan fashin mai suna Hassan Iliya, mai shekara 35 da ke Alhazawa a ƙaramar hukumar Musawa ta Jihar Katsina

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai