Kungiyar Editoci suna gabatar da babban taro don zaben sababbin shuwagabanninsu

A Yau Juma’a, Kungiyar Editoci  ke gabatar da babban taro don zaban sababbin Shugabanni da za su jagoranci Kungiyar na shekaru biyu.

Taron wanda ake gudanarwa a Owerri ta Jihar Imo, zai samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima wanda zai yi bikin bude shi, yayin da Gwamna jihar Imo Hope Uzodimma zai kasance a matsayin Mai masaukin baki.

Kimanin Editoci 400 – 500  ake sa ran za su halarci taron don kada kuri’a.

Yan takara 26 wanda kwamitin zabe na Kungiyar ya tantance za su fafata.

Daga ciki a kwai Yan takara 2 daga Jihar Kano wanda suka hada da Muhammad Sanusi Jibrin da Umoru Ibrahim.

A yammacin yau,  a ke sa ran samun sakamakon zaben Kuma za’a rantsar da sababbin Shugabannin da aka zaba.

Post masu alaƙa

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere

Yan sanda da INEC sun yaba da yadda zaɓen Dawakin Kudu ke gudana a Kano.