Kungiyar kasashen Musulmi na gudanar da taron gaggawa kan kona Alkur’ani a Sweden

Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya OIC na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al’qur’ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

Ƙasar Saudiyya ce dai ta shirya Tattaunawar wacce za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin da ƙungiyar ta kira ”abin Allah wadai” da aka aikata.

Tuni dai ƙungiyar ta yi Allah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

Dayawan ƙasashen musulmi sun dawoda jakadunsu da ke Sweden gida domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

Post masu alaƙa

JIGAWA: ‘Yan siyasa sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben 2027

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.