Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ta dakatar zanga-zangar da ta shirya

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Nijeriya, ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a duk fadin kasar nan bayan wata ganawar sirri da ta yi da manyan jami’an majalisar dattawa.

Shugaban kungiyar, Emeka Orji, ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai.

Ya ce matakin na zuwa ne bayan wata gana wa da shuwagabannin majalisar dattawa na masu rinjaye da marasa rinjaye.

Wanda hakan ya sa aka dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi ranar Laraba,  sai dai sun sha alwashin sake duba wannan al’amari nan da sa’o’i 72.

Likitocin da ke yajin aiki tun da farko sun shirya fara zanga-zangar lumana a kowacce rana, daga ranar Laraba, idan gwamnati ta gaza biyan bukatunta.

Matakin dai ya biyo bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta ba manyan daraktocin kula da lafiya na manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su fara aiwatar da manufar “idan ba aiki, babu albashi” a kan likitocin da ke yajin aikin.

A ranar 26 ga watan Yuli ne likitocin suka fara yajin aiki, biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu.

Likitocin suna neman aiwatar da manufar karin albashi ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma wasu sauran bukatunsu.

Post masu alaƙa

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.

Kwamitin yaki da shaye-shaye da fadan daba na Kano ya nemi hadin kan hukumomin tsaro