Wani tsohon dan tawaye, Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da kungiyar CRR a Nijar

Tsohon dan tawaye kuma dan siyasa a Jamhuriyar Nijar, Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da wata kungiya da za ta yi fafutukar ganin an mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Boula ya kaddamar da kungiya mai suna the Council of Resistance for the Republic (CRR) domin neman goyon baya daga kasashen duniya don mayar da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Wannan wata alama ta nuna turjiya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a karshen watan jiya.

Post masu alaƙa

Bauchi: Matar aure ta daɓa wa mijinta wuƙa a kan waya

Ana iya kawo ƙarshen rashin tsaron arewacin Najeriya cikin kwanaki 45 – KACRAN

Ƙungiyar ɗalibai masu zanga-zangar neman sauyi ta lashe babban zaɓen ƙasar Serbia