Kwamishina ya buƙaci mataimakin Gwamnan Kano ya yi murabus daga muƙaminsa

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce zai fi dacewa mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar ba zai goyi bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.

Waiya, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Muhasa da ke Kano.

Ya yi wannan kalamai ne kan rahotannin da ke cewa mataimakin gwamnan ya yanke shawarar ci gaba da biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa gwamna Abba ya sauya sheƙa zuwa APC.

A cewarsa, saɓani a cikin gwamnati na iya haifar da rashin jituwa da rage tasirin shugabanci.

“Abin da muke fata, kamar yadda muka ga wasu kwamishinoni da ba su gamsu ba suka yi murabus, shi ma mataimakin gwamna ya ɗauki mataki idan ba ya tare da gwamna,” in ji Waiya.

Ya ce gwamnati tana buƙatar haɗin kai da manufa ɗaya domin samun nasara.

“Idan kana zaune a taron majalisar zartarwa ana tattauna yadda za a gina Kano, amma ana da shakku kan inda abubuwan da aka tattauna za su kai, to akwai matsala. Shugabanci yana buƙatar amana,” in ji Waiya.

Waiya, ya yi nuni da cewa wataƙila wani shirin siyasa ne ke tasiri kan matsayar mataimakin gwamnan, inda ya ce siyasar Kano cike take da gasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *