Fasahar Mutum-Mutumi Ya fara Yi Wa Mata Tiyata ta farko a Afrika

Wani asibiti a Legas ya fara yi wa mata tiyata da na’uran robot wanda wannan shine tiyata ta farko a Afrika ta Yamma da ake amfani da na’urar ‘Robot’.

An yi wa matan tiyatar ne ranar Lahadin da ya gabata wanda hakan ke nuna yadda aiyukkan asibitin ya fadada daga yi wa maza masu fama da cutar ‘ya’yan maraina tiyata zuwa ga lura da lafiyar haihuwa na mata.

Wani babban likita kuma shugaban asibitin TPC Kingsley Ekwueme ya ci tiyata irin haka dama ce na inganta aiyukkan likitanci a Najeriya da kewaye.

Muna binciken hanyoyin rage ciyo wa Najeriya bashi — Ministan Kuɗi

“Najeriya ita ce Kasa na farko data amince da wannan sabuwan tsarin inganta lafiya wanda bai tsaya kan maza ba kadai har da mata.

Ekwueme ya ce matar da aka yi wa tiyatan da wannan na’uran matashiya ce dake fama da karban dake kama mahaifa.

“A dalilin tiyatan a ciro manyan kaba daga cikin matashiyar sannan zuwa yanzu tana samun sauki kuma muna sa ran sallamanta yau ta koma aiki gobe.

Cikin sa’o’i 6 bayan tiyatan da zaran mun tabbatar kowani bangaren jikin mutum na aiki yadda ya kamata mutum zai iya cin abinci Kuma har mu sallame shi.

An kashe wutar da wasu gungun yan daba suka kunna a unguwar Rijiya Biyu Kano

Ya ce tiyata irin haka dabara ce dake taimakawa wajen ceto rayukan mata masu fama da matsalolin karban dake kama mahaifa da juna biyu dake zama a waje daga mahaifa ‘etopic pregnancy’.

Ekwueme ya ce asibitin TPC ta yi wa matar tiyatan kyauta sannan yayin kira ga mata masu fama da irin wannan matsala da su gaggauta zuwa asibiti domin rashin neman magani ne ke hadassa matsaloli da yawan kashe kudi.

Ya ce asibitin za ta hada hannu da gwamnatin jihar Imo domin tabbatar da an kafa asibitin da na’uran robot za su rika yi a mutane tiyata a jihar.

Wani babban likita asibitin LASUTH Yusuf Oshodi ya ce matar da aka yi wa tiyatan na da shekarar 30 sannan an zabe ta bayan an gudanar da bincike.

An kashe wutar da wasu gungun yan daba suka kunna a unguwar Rijiya Biyu Kano

“Tiyatan na bin tsarin da ke cire cutar dake cikin mutum ba tare cutar da wani bangaren jikin mutum ba.

Oshodi ya ce mata kashi 70 a wasu kauyuka a kasar nan na fama da matsalolin karban ciki inda kashi 10% zuwa 20% ne ke samun alamun cutar wanda hakan ya sa da dama daga cikin su basa zuwa asibiti domin samun magani ba.

Ya ce rashin samun magani ka iya hadassa rashin jini, cututtukan dake kama zuciya.

‎‎likitan ya yi kira ga mata da su rika zuwa asibiti suna duba kansu musamman idan har suna ganin alamun da suka hada da yawan zuban jini wajen yin al’ada cewa yin hakan zai taimaka wajen guje wa samun matsaloli da ceto rayukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *