• Home  
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya raba tallafin ₦8,431,768.80 ga iyalan yan sandan da suka rasu.
- Babban Labari

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya raba tallafin ₦8,431,768.80 ga iyalan yan sandan da suka rasu.

Rundunar ‘ƴan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin , CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta raba Cek ɗin kuɗi Naira miliyan takwas da dubu ɗari 431 da 768 da kobo 80 (₦8,431,768.80) ga iyalan jami’an rundunar 18 da suka rasu. Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar CSP Abdullahhi Haruna Kiyawa, ya bayyana ta cikin wata […]

Rundunar ‘ƴan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin , CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta raba Cek ɗin kuɗi Naira miliyan takwas da dubu ɗari 431 da 768 da kobo 80 (₦8,431,768.80) ga iyalan jami’an rundunar 18 da suka rasu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar CSP Abdullahhi Haruna Kiyawa, ya bayyana ta cikin wata sanarwa da rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce wannan wani ɓangare ne na bikin ranar ƴan sanda ta shekarar 2026, a tsarin tallafin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya GP Olatunji Rilwan Disu, don kula da walwalar ƴan sanda da iyalansu musamman waɗanda sukaji rauni ko kuma suka rasu a bakin aiki.

CP Bakori ya shawarci waɗanda suka amfana da tallafin su yi amfani dashi yadda ya dace, tare da yin addu’a ga mamatan.

Anasu ɓangaren waɗanda suka samu tallafin sun bayyana godiyarsu da kuma farin cikin kan yadda rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta jajirce wajen kula da rayuwarsu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai