Kwamishinan ƴan sandan Kano, CP I.A. Bakori ya gargaɗi dakarunsa su guji shiga harkokin siyasa.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi jami’an rundunar da su guji shiga harkokin siyasa ko nuna goyon baya ga kowace jam’iyya, tare da mayar da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

CP Bakori ya yi wannan gargaɗi ne yayin ganawarsa da jami’an Area Command ta Tarauni, a ci gaba da rangadin da yake yi a sassan jihar.

Ya kuma buƙaci jami’an da su yi amfani da shafukan sada zumunta yadda ya kamata, yana mai jaddada cewa jami’an ƴan sanda ba ƴan siyasa ba ne.

Haka zalika, ya nuna damuwa kan wani jami’in da aka gani a wani faifen bidiyo, inda yake nuna murna bayan zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Bagwai da Shanono a watannin baya dake jihar Kano.

Kwamishinan ya ce rundunar ’yan sandan Nijeriya ba ta da wata jam’iyya sai kare doka da kuma hidimtawa ƙasa.

 

Post masu alaƙa

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC