Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya raba tallafin ₦8,431,768.80 ga iyalan yan sandan da suka rasu.

Rundunar ‘ƴan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin , CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta raba Cek ɗin kuɗi Naira miliyan takwas da dubu ɗari 431 da 768 da kobo 80 (₦8,431,768.80) ga iyalan jami’an rundunar 18 da suka rasu.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar CSP Abdullahhi Haruna Kiyawa, ya bayyana ta cikin wata sanarwa da rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce wannan wani ɓangare ne na bikin ranar ƴan sanda ta shekarar 2026, a tsarin tallafin babban sufeton ƴan sandan Nijeriya GP Olatunji Rilwan Disu, don kula da walwalar ƴan sanda da iyalansu musamman waɗanda sukaji rauni ko kuma suka rasu a bakin aiki.

CP Bakori ya shawarci waɗanda suka amfana da tallafin su yi amfani dashi yadda ya dace, tare da yin addu’a ga mamatan.

Anasu ɓangaren waɗanda suka samu tallafin sun bayyana godiyarsu da kuma farin cikin kan yadda rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta jajirce wajen kula da rayuwarsu.

Post masu alaƙa

A riƙa yi wa masu shirin aure gwajin miyagun ƙwayoyi :- Buba Marwa

Bwala yayi zargin akwai hannun kasashen wajen kan matsalar tsaro a Nijeriya

Dakarun yan sanda 200 sun samu horon sarrafa makami a Kano.