Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tattauna da ƙungiyoyi don magance tada tarzoma a lokutan zaɓe.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta gana da ƙungiyoyin farar hula (CSOs) domin tattauna hanyoyin hana tashin hankali a lokutan zaɓe, a wani ɓangare na bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026.

Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa  da wayar da kai kan illar tayar da hankalin al’umma a lokutan zabe, tare da ƙudirin tabbatar da zaman lafiya.

Masu ruwa da tsaki sun yaba da wannan yunƙuri tare da yin alƙawarin bada goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .