Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba da haɗin kan da jama’a suke ba su

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ziyarci yankunan Bichi da Dambatta domin duba halin tsaro da ƙarfafa haɗin kai tsakanin ’yan sanda da al’umma.

CP Bakori ya yaba da goyon bayan da jama’a ke bayarwa musamman wajen basu bayanan sirri, inda ya  buƙace su ci gaba da kai rahoton abubuwan da basu amince da sub a ga ofishin yan sanda mafi kusa.

Ya kuma hori jami’an ’yan sanda da su yi aiki cikin gaskiya da nuna ƙwarewa da kuma mutunta haƙƙin jama’a.

Shugabannin al’umma da shugabannin gargajiya sun yaba da ziyarar tare da alƙawarin ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

Post masu alaƙa

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama dan bindiga da sanye da kayan sojoji.

Majalisar Wakilai ta janye kudirinta kan ‘yan sandan jihohi tare da yin nazari kan buƙatar Tinubu