APC za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa a gobe Asabar

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da zaɓen fitar da gwanin takarar shugaban ƙasa a gobe Asabar ta hanyar ƴartinƙe.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce za a gudanar da zaɓukan a faɗin mazaɓun ƙasar 8,809.

Shugaba Tinubu da Stanley Osifo ne ke neman tikitin tsayawa jam’iyyar takara a zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce duk wanda ke da katin rajistar jam’iyyar na da damar zaɓar wanda zai yi wa jam’iyyar takara.

Sanarwar ta ce za a tattara sakamakon zaɓukan kowace mazaɓa a ƙaramar hukuma, kafin akai shi babban cibiyar tattara sakamakon ta ƙasa da ke Abuja.

Jam’iyyar ta kuma naɗa tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Pius Anyim Pius a matsayin shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasar.

Yayin da ta naɗa Sanata Ali Ndume a matsayin shugaban kwamitin ƙarɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen.

Post masu alaƙa

Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri

Najeriya ta ƙaddamar da yaƙi ta sama kan ƴan fashin daji

Sojoji sun ceto mutum 4 bayan shafe shekara 3 a hannun Boko Haram