Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Ziyarci Wuraren Da Aka Girke Jami’an Tsaro Don Dakile Barazanar Yan Bindiga.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa suna da kyakkyawar dangantaka da sauran hukumomin tsaro dake a jihar.

CP Ibrahim Bakori, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman don duba jami’an tsaron da aka girke, a wuraren da ake zargin yan bindiga na yiwa mazauna kananan hukumomin da suke iyaka da jihar Katsina barazanar garkuwa da su da kuma satar shanu.

Kwamishinan ya duba jami’an yan sanda da sojojin da aka girke a garuruwan, Faruruwa da kuma Garin Tsaure dake karamar hukumar Shanono, tare da karfafa musu gwiwa, wajen ci gaba da tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Bakori, ya ziyarta ofishin yan sandan kananan hukumomin, Ghari da Tsanya kafin ya isa garuruwan, Faruruwa da Tsaure a karamar hukumar Shanono.

Ya kara da cewa watan da ya gabata mutanen garuruwan duk yan bindiga sun firgita su, amma yanzu sun dawo gidajensu sakamakon samar da jami’an tsaro da aka yi.

Sai ya bukaci jami’an su kara jajircewa da kuma yin aiki tare ba tare da rabuwar kai ba, inda ya yi kira ga jama’a su ci gaba da taimaka musu ta hanayar basu bayan sirri wanda zai taimaki harkar tsaro.

 

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere