• Home  
  • Kwankwaso ya zargi Abba da amfani da EFCC don ɓata masa suna
- Labarai

Kwankwaso ya zargi Abba da amfani da EFCC don ɓata masa suna

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɓata masa suna da kuma raunana damar jam’iyyarsa ta NDC a zaɓen 2027. A cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Jumaʼa, Sanata Kwankwaso ya ce […]

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɓata masa suna da kuma raunana damar jam’iyyarsa ta NDC a zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Jumaʼa, Sanata Kwankwaso ya ce yana zargin gwamnan da ƙoƙarin shigar da shi da iyalansa cikin ce-ce-ku-ce ta hanyar amfani da Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa, EFCC.

Tsohon ministan ya kuma ce Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya taɓa aiki a ƙarƙashinsa a matsayin mataimaki na musamman, babban sakataren sirri da kwamishina, ya yi amfani da amincewar da ya samu a tsakaninsu wajen samun bayanan da yake zargin ana amfani da su wajen ɓata masa suna.

Duk da dai ba a fito da wata shaida ta fili ba, Sanata Kwankwaso ya kuma yi zargin cewa gwamnan ya gabatar da wata buƙata ga EFCC watanni da suka gabata domin hukumar ta bincike shi, amma bayan abin da ya bayyana a matsayin rashin nasarar wannan yunƙuri, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative, wato SACGGI, wajen matsa wa hukumar lamba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000