Ma’aikatan Jinya Sun Dakatar Da Yajin Aiki A Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce ma’aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi.

Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma’a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin tarayya bayan wata ganawa a yau ɗin.

A ranar Talata ne ma’aikatan jinyar suka fara yajin aikin saboda abin da ƙungiyar tasu ta bayyana da “gazawar gwamanti wajen biyan buƙatunsu cikin wa’adin kwana 15 da ta bayar” ranar 14 ga watan Yuli.

Akaasrin buƙatun sun jiɓanci walwalar ma’aikata, da alawus-alawus a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriya.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya