Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa.
Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.1 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025.
Hakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke cikin barazanar yunwar.
Ofishin Majalisar mai kula da Agaji (UNOCHA), a rahotonsa na mai taken “Najeriya a 2025 bukatun agajinta da kuma hanyoyin magance su” ya yi bayani daki-daki kan kalubalen da ake fuskanta a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.
- Rundunar Sojin Ruwan Najeriya Za Ta Kafa Sansani A Kebbi
- Kananan Ma’aikata Ne Suka Ci Zarafin Wakilan Tashar MUHASA TVR- KNUPDA
Rahoton ya ce akwai akalla yara miliyan daya da dubu 800 da kef ama da matsanancin karancin abinci.
Rahoton ya alakanta hakan da ci gaba da karuwar farashin kayayyaki a Najeriya wanda ya kai kaso 40.9 cikin 100 a watan Yunin 2024.
Kazalika, karuwar adadin na da nasaba da rage tallafin da MDD ke bayarwa ba, sanadiyyar yanke mata kudaden tallafin da musamman Amurka ke bayarwa.