lafiya

Yajin Aiki: NARD Za Ta Yi Zanga-Zangar Lumana A Zariya

Ƙungiyar Likitoci Masu Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aiki na ƙasa da aka shirya fara wa a ranar 12 ga watan Janairu, 2027. Wannan ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta cimma […]

Read more

Kano Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Shan Inna

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta tabbatar da gano sababbin nau’o’i guda huɗu na ƙwayar cutar shan inna a jihar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ci gaba da yin rigakafin yadda ya kamata ba, kwayar cutar na iya sake yaɗuwa bayan an kawar da ita. Farfesa Salisu Ahmad, […]

Read more

Muna Buƙatar Masu Fassara A Asibitoci : Kurame

Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. […]

Read more

Ma’aikatan Jinya Sun Dakatar Da Yajin Aiki A Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce ma’aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi. Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma’a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin […]

Read more