Mahaifin Umar, guda daga cikin matasan da a ke zargi da yi wa Fatima Abubakar kisan gilla, da ya’yanta 6, a unguwar Chiranci Dorayi gidan Kwari, da ke karamar hukumar Kumbotso a Kano, ya ce, ba zai je kotu a yayin shari’a a kan zargin da a ke yi wa ɗan na sa ba.
Mahaifin matashin mai suna, Mallam Auwal, ya bayyana hakan lokacin da ya ke nuna damuwar sa kan abinda a ke zargin ɗansa da aikata wa, yayin zantawar sa da Freedom Radio, a ranar Litinin.
Ya kuma ce, abinda dan na sa ya aikata ya matukar tayar masa da hankali, ya na mai cewa, kamata ya yi a hukunta ɗansa, tare da dukanin sauran masu aikata laifi irin na sa, domin ya zama izina.
“Ni da Matata ba za mu je zaman shari’ar da za a yi a kan zargin da a ke yi wa ɗan mu na kisan gillar Fatima Abubakar, da ya’yanta 6 ba, sai dai ko idan hukuma ce ta ce na je, in ji shi.”
Malam Auwal, ya kuma yi zargin cewar, ɗan na sa na da hannu a kisan da a ka yi wa karamar ƴarsa a kwanakin baya, inda ya kuma yaba wa jami’an tsaro, bisa kokarin da su ka nuna wajen kamata wadanda a ke zargi da aikata kisan gillar.
A cewar sa “Bai dace a rinƙa barin irin masu halayya irin su Umar ba, su na zama suna cike guri tare da cinye abincin gwamnati, bayan kuma ba su da amfani, in ji shi.”
Ya ce, abinda ya aikata wa kanwar sa, da ya’yanta su 6, da kuma kanwar Matar sa da kishiyar ta, da karamar ‘yarsa da ya ke zargin ɗan nasa da kashewa, kamata ya yi a je a hukunta shi, da sauran masu halayya irin ta sa.
A ranar Asabar 17 ga Jnairu, 2026, ne dai aka yi wa Fatima Abubakar mai shakaru 35, kisan gilla da ya’yanta 6, a cikin unguwar ta Chiranci gidan Kwari, ko da ya ke, tuni runudnar ‘yan sandan jihar Kano, ta bayyana kama uku daga cikin wadanda ake zargi.