Mahaifiyar Nasir El-Rufai ta rasu

Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai mai suna Hajiya Umma El-rufai ta rasu.

Ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai ne ya sanar da rasuwar a ranar Juma’a, inda ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Ina sanar da al’umma cewa Allah ya yi wa kakata, Hajiya Umma El-Rufai rasuwa,” in ji shi.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar Malam Nasir El-Rufai. “Muna godiya ga Allah bisa rayuwar da ta yi. Muna addu’ar Allah ya jiƙanta da rahama. Muna buƙatar addu’arku a gare ta,” in ji shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan ke tsare a hannun hukumar ICPC, inda ake ci gaba da gudanar da shari’a kan zarginsa da badaƙala a lokacin da yake gwamnan jihar Kaduna.

Post masu alaƙa

Tinubu ya tafi hutun mako uku

Tinubu ya nemi kotu a Amurka ta hana fitar da takardun zarginsa da safarar ƙwaya’

Tinubu da gwamnoni sun kafa kwamitin lalubo hanyoyin rage tsadar sufuri