Fiye da wakilai 8,000 da gwamnonin APC 31 na shirin halartar taron APC

Aƙalla wakilai 8,433 daga sassan Najeriya daban-daban ne tare da gwamnoni 31 ne ake sa ran za su halarci babban taron ƙasa na jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Shugaban ƙasar Bola Tinubu da ministocinsa da ma gwamnonin jam’iyyar 31 ne za su jagoranci taron.

Jam’iyyar za ta zaɓi shugabannin da za su jagorance nan da shekara huɗu masu zuwa.

Tuni dai jam’iyyar ta sanar da aniyar amfani da hanyar masalaha wajen zaɓen sabin shugabannin nata.

Cikin waɗanda ke takarar har da shugaban riƙon jam’iyyar na yanzu, wanda tuni aka tantance domin tsayawa takarar.

Haka ma wasu bayanai na ambato tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Almakura.

Fiye da wakilai 8,000 da gwamnonin APC 31 na shirin halartar taron APC

Post masu alaƙa

Ƴan sandan Kano za su ƙara ƙaimi wajen amsa kiran gaggawa – CP Bakori

Masu Garkuwa Da Janar Rabe Na Neman A Sako ’Yan Bindigar Da Ke Hannun Gwamnati

Gwamna Namadi ya dakatar da hadimansa huɗu