Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci ta nuna takaici kan sauyi a dokar haraji

Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ta ce ta yi takaici dangane da zargin da ake ta yaɗawa cewa akwai banbanci tsakanin dokar haraji da ake son aiwatarwa a watan Janairun 2026 da wadda ƴan majalisar ƙasar suka amince.

A wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta ce idan dai har hakan ya tabbata to babu abin da zai haifar illa janyo yanke ƙauna da raini daga al’ummar ƙasa.

Majalisar ta ƙara da cewa dalilin da ya sa al’amarin ya ba ta takaici shi ne sakamakon irin gudunmowar da ta bayar ga kundin na dokar harajin ƙasa.

Daga ƙarshe majalisar ta nemi ɓangarorin biyu na zartarwa da majalisar dokoki da su yi bincike domin gano yadda aka yi aka samu sauye-sauyen.

Post masu alaƙa

CP Bakori ya umarci kwamandojin yan sanda su ƙara kaimi wajen yaki da laifuka a Kano.

Kano: Gini Ya Rufta Kan Mutane 16 Ciki Har Da Yara Shida

KACRAN: Babu wani babban rikicin manoma da makiyaya a Yobe