Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Amince Da Karin Naira Biliyan 215.3 A kasafin Kudin 2025

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira biliyan 215.3 bayan tattaunawar da ƴan majalisar suka gudanar a zaman majalisa na yau Litinin.

Wannan amincewa ta biyo bayan buƙatar da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika, inda Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranci zaman.

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalissar , Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa jimillar kuɗin ƙarin kasafin ya kai ₦215,378,374,543.62.

Kakakin ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa za su sa ido sosai wajen aiwatar da kasafin, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da hukumomi za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Majalisar ta amince da kudirin bayan doguwar muhawara da kuma duba cikakken bayani daga mambobi kafin ƙarshe ta zartar da shi a matsayin doka.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya