Majalisar Jihar Neja Ta 10 Ta Gayyaci Hukumomin Tsaron a Zamanta Na Farko

Sabuwar Majalisar Dokokin jihar Neja ta 10 ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin jin bahasi daga wajensu akan matsalar rashin tsaron da ke kara kamari a jihar.

Sabon shugaban Majalisar Dokokin jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce, a yau Laraban ne za su gana da shugabannin hukumomin tsaron dake aiki a jihar wanda hakan shi ne zaman aiki na farko da za su fara yi bayan kaddamar da majalisar a jiya Talata.

A baya dai an sha zargin ‘yan Majalisun jihohin da zama ‘yan amshin shata ga bangaren gwamnoni bisa la’akkari da yadda suke zama tamkar rakumi da akala a tsakaninsu da banagaren zartarwar.

To sai dai, shugaban Majaliasar Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce a wannan karon za su hada hannu da bangaren zartarwa wajan kawo ci gaba mai amfani ga Al’umma.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaƙi da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Kano

Mutane uku sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

CP Ibrahim Bakori ya kaddamar da sabon ofishin yan sanda a Falgore.