Rikicin Shugabanci Ya Tilasta Dakatar da Rantsar da ‘Yan Majalisar Jihar Jigawa

Rashin samun daidaito game da wanda zai jagoranci majalisar jihar Jigawa karo na takwas, ya haifar da tsaiko wajen rantsar da sabbin ‘yan majalisar a jiya Talata.

Takaddamar ta kaure tsakanin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar cikin su har da tsohon gwamnan jihar Badaru Abubakar, dangane da zaben shugaban majalisar dokokin jihar.

Post masu alaƙa

Jirgin sojin Najeriya ɗauke da mutum 32 ya faɗi a Ondo

Yaushe aka fara gano man fetur a Najeriya?

Matasan Arewa sun bukaci gwamnonin arewa maso gabas su fi bai wa tsaro da samar da aikin yi muhimmanci